Acts 22

1“ʼYanʼuwa da iyaye, ku saurari kāriyata yanzu.” 2Da suka ji ya yi musu magana da Aramayik, sai suka yi tsit. Sai Bulus ya ce, 3“Ni Bayahude ne haifaffen Tarsus na Silisiya, amma a nan birnin ne aka rene ni. Aka horar da ni sosai cikin dokokin kakanninmu a ƙarƙashin Gamaliyel ni ma dā mai himma ne cikin bauta wa Allah kamar yadda kowannenku yake a yau. 4Na tsananta wa masu bin wannan Hanyar har ga mutuwarsu, ina kama maza da mata ina kuma jefa su cikin kurkuku, 5kamar yadda babban firist da dukan Majalisa za su iya shaida. Na ma karɓi wasiƙu daga gare su zuwa ga ʼyanʼuwansu a Damaskus, na kuma tafi can don in kawo waɗannan mutane a ɗaure zuwa Urushalima don a hukunta su.

6“Wajen tsakar rana da na yi kusa da Damaskus, ba zato ba tsammani sai wani babban haske daga sama ya haskaka kewaye da ni. 7Sai na fāɗi a ƙasa na kuma ji wata murya ta ce mini, ‘Shawul! Shawul! Don me kake tsananta mini?’

8“Sai na yi tambaya na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’

“Ya amsa ya ce, ‘Ni ne Yesu Banazare, wanda kake tsanantawa.’
9Abokan tafiyata suka ga hasken, amma ba su fahimci muryar mai magana da ni ba.

10“Sai na yi tambaya, na ce, ‘Me zan yi, ya Ubangiji?’

“Ubangiji ya ce, ‘Tashi, ka tafi cikin Damaskus. A can za a faɗa maka duk abin da aka shirya za ka yi.’
11Abokan tafiyata suka ja ni a hannu zuwa cikin Damaskus, saboda ƙarfin hasken ya makanta ni.

12“Wani mutumin da ake kira Ananiyas ya zo ya gan ni. Shi mai ibada ne wajen kiyaye dokoki wanda dukan Yahudawan da suke zama a can suna girmama shi ƙwarai. 13Ya tsaya kusa da ni ya ce, ‘Ɗanʼuwa Shawul, ka sami ganin garinka!’ A daidai lokacin kuwa na iya ganinsa.

14“Saʼan nan ya ce, ‘Allah na kakanninmu ya zaɓe ka ka san nufinsa ka kuma ga Mai Adalcin nan ka kuma ji kalmomi daga bakinsa. 15Za ka zama mai shaidarsa ga dukan mutane game da abin da ka gani ka kuma ji. 16Yanzu me kake jira? Ka tashi, a yi maka baftisma, a wanke zunubanka, ta wurin kira bisa ga sunansa.’

17“Saʼad da na dawo Urushalima ina cikin adduʼa a haikali, sai na ga wahayi 18na ga Ubangiji yana magana. Ya ce mini, ‘Maza! Ka bar Urushalima, gama ba za su yarda da shaidarka game da ni ba.’

19“ Na amsa na ce, ‘Ubangiji, waɗannan mutane sun san cewa na bi majamiʼa-majamiʼa na jefa waɗanda suka gaskata da kai a cikin kurkuku, in kuma yin musu dūka. 20Saʼad da kuma aka zub da jinin Istifanus mashaidinka, na tsaya can ina ba da goyon bayana ina kuma tsaron tufafin masu kisansa.’

21“Saʼan nan Ubangiji ya ce mini, ‘Je ka; zan aike ka can nesa a wurin Alʼummai.’ ”

Bulus Ɗan Ƙasar Roma

22Taron suka saurari Bulus sai da ya yi wannan magana. Saʼan nan suka ɗaga muryoyinsu suka yi ihu suka ce, “A raba duniya da wannan mutum! Bai cancanci yǎ rayu ba!”

23Da suna ihu suna kaɗa mayafansu suna da ta da ƙura sama, 24sai shugaban ƙungiyar sojan ya umarta a kai Bulus a barikin soja. Ya ba da umarni a yi masa bulala a kuma tambaye shi abin da ya sa mutane suke masa ihu haka. 25Suna kwantar da shi ke nan domin a yi masa bulala, sai Bulus ya ce wa jarumin da yake tsaye a nan, “Ashe, daidai ne bisa ga doka a yi wa ɗan ƙasar Roma bulala wanda ba a ma tabbatar da laifi a kansa ba?”

26Da jarumin ya ji haka sai ya je wurin shugaban ƙungiyar sojan ya ce masa, “Me kake so yi ne? Wannan mutum ɗan ƙasar Roma ne.”

27Sai shugaban ƙungiyar sojan ya je ya tambayi Bulus ya ce, “Faɗa mini, kai ɗan ƙasar Roma ne?”

Bulus ya ce, “I.”

28Sai shugaban ƙungiyar sojan ya ce, “Sai da na biya kuɗi mai yawa kafin in zama ɗan ƙasa.”

Bulus ya ce, “Ni kuwa an haife ni ɗan ƙasa.”

29Waɗanda dā suke shirin yin masa tambayoyi suka ja da baya nan da nan. Shugaban ƙungiyar sojan kansa ya tsorata da ya fahimci cewa ya sa wa Bulus, ɗan ƙasar Roma sarƙa.

A Gaban Majalisa

30Washegari da yake shugaban ƙungiyar sojan ya so yǎ tabbatar da ainihin abin da ya sa Yahudawa suke zargin Bulus, sai ya sake shi ya kuwa umarci manyan firistoci da dukan Majalisar su taru. Saʼan nan ya kawo Bulus ya sa ya tsaya a gabansu.

Copyright information for HauSRK